Breaking News

2023: Timi Frank Ya Gargadi Wakilan Zabe Na PDP Akan Siyar Da Kuri'u

Kwamared Timi Frank

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Tsohon Mataimakin Sakataren Yada Labaran jam’iyyar APC na kasa, Kwamared Timi Frank, ya gargadi wakilan da suka gabatar da kudurin zabar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a babban taronta na musamman na kasa da za a gudanar a ranar Asabar, da ka da su kuskura su sayar da kuri’unsu ga mafi wadanda suka fi bayar da kudi.

Frank a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya bukaci wakilan zaben da su fifita ci gaban Nijeriya da ci gaban kasa sama da duk wani buri na bangaranci, son kai na yau da kullum ta hanyar zaben dan takarar da ke da tarihin gudanar da aiki tare da samar da mafita, kyakkyawan shugabanci, kwarewa, cancanta, halayya mai kyau da kuma kyakkyawan kuduri na siyasa.

A cewarsa, wannan kiran ya zama wajibi domin a samar da tsarin da zai sake kawo ci gaban kasa tun daga shekarar 2023.

Ya jaddada cewa wakilan zaben jam’iyyar PDP a yanzu suna da aikin da ya dace na ganin sun yi abin da ya dace domin gyara tabarbarewar arzikin kasar nan wanda ake fama da shi sakamakon rashin alkiblar jam’iyyar APC inda rudani, rashin tsarin dimokuradiyya na cikin gida da dora ‘yan takara suka zama ka’idoji da tsare-tsare na jam’iyyar.

Frank, wanda shi ne jakadan United Liberation Movement for West Papua (ULMWP) a Gabashin Afirka da Gabas ta Tsakiya, ya ce: “Mun lura cikin matukar takaici cewa a lokacin zabukan fidda gwani na ‘yan majalisar wakilai, da majalisar Dattawa da na gwamnonin PDP, masu rike da mukaman siyasa, musamman Gwamnoni masu barin gado, sun yi sace tsarin ne ta hanyar dora wa jama’a na su.

Frank, wanda shi ne Jakadan ‘United Liberation Movement For West Papua (ULMWP)’ a Gabashin Afirka da Gabas ta Tsakiya, ya ce: “Mun lura da matukar takaici cewa a lokacin zabukan fidda gwani na ‘yan majalisar wakilai, da majalisar dattawa da na gwamnonin PDP, ofishin siyasa masu rike da mukamai, musamman Gwamnoni masu barin gado, sun yi awon gaba da tsarin ne ta hanyar dora wa jama’a nasu.

 “Mun kuma ga yadda masu rike da mukaman siyasa ke tsoratarwa, cin zarafi da kuma amfani da makudan kudade da ake ganin sun wawure wajen ba wa wakilai cin hanci da rashawa.

“Wannan mataki da Gwamnonin suka dauka ba shakka ba zai haifar da irin shugabancin da ‘yan Nijeriya ke so ba a zabe mai zuwa wanda zai fara daga zaben 2023 mai zuwa.

“Saboda haka, muna kira ga wakilai da kakkausar murya da suka halarci babban taro na musamman na PDP da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a ranar Asabar da su gujewa duk wani nau’in cin hanci da rashawa amma su zama jajirtattu wajen zaben dan takarar da ya cancanta ya jagoranci kasarmu baki daya domin ya fitar da ita daga duhun da ta afka.

“Kasarmu na cikin mawuyacin hali sakamakon rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki, sannan kuma sai mutum mai kwazo, gogewa da sanin makamar salon siyasar zamani da yanayin zamantakewar al’umma yakamata a zaba a matsayin wanda zai rike tutar jam’iyyar.

"Wakilan zaben ka da su kalli jin daɗin rana ɗaya ko ribar rana daya, su karbi ɗimbin kuɗin da aka kawo musu, su zaɓi dan takara mara kyakkyawan dabi’a da rashin cancanta wanda a ƙarshe zai lalata makomarsu da ta ƙasar baki ɗaya.

“Madalla, ’yan Nijeriya sun san sunaye da adireshi na wadannan wakilai na zabe kuma tabbas za su bayyana su bayan kammala taron ko dai a matsayin wadanda suka kada kuri’ar ceto kasar nan a daidai lokacin da ake fama da rikice-rikice a kasar, ko kuma wadanda suka yi zabe domin Aljihunsu suka sake jefa kasar nan cikin mawuyacin hali na rashin fata, rashin aikin yi, rashin tsaro, yunwa, fidda rai, cututtuka da rugujewar al’umma da ba za a iya jurewa ba.

Halin da kasar nan ta shiga na mawuyacin hali a karkashin Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) wanda yake jagorantar gwamnatin APC ya samo asali ne sakamakon rashin kyakkyawan zabi da wakilan jam’iyyar APC suka yi a shekarar 2014 a irin wannan babban taron kasa na zaben dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Ya kara da cewa: “Muna inda muke a yau domin a baya wakilai sun sayar da kuri’unsu don kudi, addini, kabilanci da kuma son zuciya.

“A bayyane yake cewa kalubalen da ke tattare da durkushewar tattalin arziki, rashin tsaro da ya ki ci yaki cinyewa, yunwa, rashin aikin yi, matsalar wutar lantarki da yaki karewa, da kuma rashin ilimi da ke addabar kasar nan aiki ne kai tsaye na zaben ‘yan takara musamman na ofishin shugaban kasa da wakilan jam’iyyun siyasa suka yi tun bayan komawar kasar mulkin dimokradiyya a shekarar 1999.

“Wakilan zabe a yau suna bigiren tarihi don zabar dan takara wanda idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa zai nade hannayensa da zuciyarsa ya yi wa kasar nan aiki ba tare da nuna bangaranci ba.

“Wadannan wakilan zaben dole ne su sanya Nijeriya a gaba. A baya su ne ke da alhakin haifar da munanan shugabanci a kasar nan, domin wadanda suka zaba a lokacin zabukan fidda gwani sun zama zabi daya tilo da ‘yan Nijeriya za su zaba a lokacin babban zabe.”

Ya bukaci wakilan zaben da su nuna jarumtaka su bijirewa duk wani nau'i na tsoratarwa, magudi da karkatar da Gwamnoni masu barin gado wadanda suke taimaka musu wajen ganin sun zama wakilai ta hanyar nuna kishin kasa wajen zaben ’yan takara masu cancanta da nagarta wadanda a karshe za su amsa addu’ar ‘yan Nijeriya idan aka zabe su a lokacin babban zabe.

Ya tunatar da su cewa a yanzu Gwamnonin da suke tunzura su don biyan bukatunsu na son rai ba za su sha wahala ba idan wani mugun shugaba ya sake fitowa daga zabin da suka zaba domin shugabannin jihohin da ke barin gadon tuni sun tara dukiya mai yawa a bisa ka’ida da kuma ba bisa ka’ida ba da zai ciyar da su da iyalansu na tsawon lokaci.

“A don haka, wakilan zaben su ma za su wahala da fuskantar mummunan sakamako na sayar da kuri’unsu ga ’yan takarar da ba su dace ba don samun kudi wanda ke da matukar tasiri.

"Wannan dama ce ga wakilan zaben don kafa tarihi. Gwara a ce sun zo ne don ceton al'umma da kuri'unsu a daidai irin wannan wannan mawuyacin lokaci a wani irin nau’in sauyi. Dole ne su guji cewa 'da na sani' nan gaba kadan," in ji shi.

Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi wa wakilan da za su halarci babban taron jam’iyyar PDP lamba tare da dora musu alhakin da ya kamata idan suka zabi dan takarar shugaban kasa wanda zai kara tabarbare yanayin rayuwa da ba za a iya jurewa da shi ba ko kuma wanda kasar za ta dan sarara bayan fitowar wanda zai zama shugaban kasa.

SA HANNU


Kwamared Timi Frank

ULMWP Jakadan Gabashin Afrika da Gabas ta Tsakiya

No comments

Drop Comment